APC a Yobe ta ayyana Baba Malam Wali a matsayin zabin ɗan takara na gwamna a 202.
Daga Hassan Ahmed Maibaru.
Dandalin manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Yobe ya ayyana tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali, a matsayin zabin ɗan takararta na gwamna a zaben shekarar 2027.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana Malam Wali a matsayin gogaggen kwararre mai cikakken ilimi, hakuri da kuma halin shugabanci da suka dace da kyakkyawan jagoranci da gudanar da mulki.
Dandalin ya kuma lura cewa tsohon SSG din ya dade yana taka rawa a gwamnatoci daban-daban na jihar tsawon shekaru, lamarin da ke ba shi cancantar ci gaba da aiwatar da manufofi da hangen nesa na ci gaban jihar.
A yayin taron, jam’iyyar ta amince da amfani da tsarin maslaha (consensus) wajen fidda ‘yan takararta a zabukan da ke tafe.
Hakazalika, jam’iyyar ta amince da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2027.
Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, tare da shugaban dandalin masu ruwa da tsaki na jihar, Sanata Ibrahim Gaidam, sun jaddada kudirin jam’iyyar na ci gaba da tattaunawa domin karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar.

