Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sake jaddada aniyarsa ta ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar daidaita shugabanci da muradun al’umma, inda ya yi alƙawarin goyon bayan buƙatar al’ummar Yamaltu/Deba na samar da sanata na gaba daga Gombe ta Tsakiya a zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓar wata tawaga daga Yamaltu/Deba a Fadar Gwamnati da ke Gombe. Tawagar ta ƙunshi sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, masana da kuma wakilan matasa da mata.
Da yake jawabi a madadin tawagar, jagororinsu sun roƙi gwamnan da ya mara musu baya domin tabbatar da adalci a wakilcin mazabar Gombe ta Tsakiya, wadda a halin yanzu Mohammad Danjuma Goje ke wakilta.
Sun bayyana cewa kujerar sanatancin ta daɗe tana hannun Ƙaramar Hukumar Akko, don haka akwai buƙatar a samar da daidaito, adalci da haɗa kai wajen rabon muƙaman siyasa a yankin.
A nasa jawabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatar da goyon bayansa, yana mai cewa buƙatar tasu ta dace kuma ta cancanci a saurare ta. Ya ƙara da cewa dimokuraɗiyya dole ne ta wakilci muradin jama’a, tare da jaddada cewa shugabancinsa na bai wa kowa dama da muhimmanci.
END
The 301 Artillery Regiment (General Support) of the Nigerian Army has announced that it will conduct its first 2026 Range Classification Exercise on Monday and Tuesday at the Small Arms Range in Liji, Gombe State.
Acting Assistant Director, Army Public Relations, Lieutenant Kingsley Ugwuoke, advised residents of Liji in Yamaltu/Deba Local Government Area not to panic at the sound of gunshots during the exercise.
He explained that the drill is a routine bi-annual training aimed at refreshing soldiers’ skills and improving weapon handling for effective military operations.
END
Rundunar Sojin Najeriya ta 301 Artillery Regiment (General Support) ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen gwajin harbi na farko na shekarar 2026 a ranakun Litinin da Talata a filin atisayen ƙananan makamai da ke Liji a Jihar Gombe.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Laftanar Kingsley Ugwuoke, ya buƙaci mazauna yankin Liji da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu/Deba da kada su firgita idan sun ji karar harbe-harbe yayin atisayen.
Ya bayyana cewa atisayen na daga cikin horo na yau da kullum da ake yi sau biyu a shekara, domin sabunta ƙwarewar sojoji da inganta iya sarrafa makamai domin samun nasara a ayyukan soja.